Skip to content
Saurari Shirye-shiryenmu
  • Game Da Mu
  • Talla
  • Tuntube Mu
GTA Hausa Logo

GTA Hausa

Amintacciyar Murya

gtahausa Banner
  • Babban Shafi
  • Labarai
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Kiwon Lafiya
  • Najeriya
  • Afrika
  • Amurka
  • Shirye-Shirye
  • Toggle search form
  • Gamayyar ADC Ta Bukaci Shugaban INEC Ya Yi Murabus Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Ƙungiyar ‘Yan Jarida (NUJ) A Bauchi Ta Yi Allah Wadai Da Mummunan Harin Da Jami’an ‘Yan Sanda Suka Kai Wa Daya Daga Cikin Mambobinta Labarai
  • An Kwace Nasarar Da Senegal Tayi na (CAF) An Ba Wa Maroko Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Zelensky: Gabas Ta Tsakiya Na Iya Nuna Makomarmu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Mojtaba Khamenei Ya Zama Sabon Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu

Dan Ra’ayin Mazan Jiya Leo Brent Zai Kyautata Alakar Afirka Ta Kudu Da Amurka
Published: February 17, 2026 at 9:49 AM | By: Aliyu Bala Gerengi

Mutumin da shugaban Amurka Donald Trump ya nada jakadan kasar a Afirka ta kudu, dan gwagwarmaya mai ra’ayin mazan jiya Leo Brent Bozell na uku, wanda kuma marubuci ne ya sauka kasar, inda zaiyi aiki domin gyara dangantaka tsakanin kasashen biyu wanda yayi tsami.

Wani jami’i a ofishin jakadancin Amurka ya fadawa kamfanin dilancin labarai na Reuters cewa, Ambasda Bozell ya iso. Kuma ana sa ran zai gabatarwa shugaba Cyril Ramaphosa takardunsa gabannin ya fara aiki.

Dangantaka tsakanin hukumomi a Washington da Pretoria sunyi baya ainun bara, yayinda Trump yake sukar kasar cewa tana muzgunawa tsiraru farar fata, ya soki mu’amalar kasar da Rasha da kuma China, sannan ya aza mata haraji mai yawa kan kayayyaki daga kasar.

Afirka ta kudu bada ta da jakada a Washington tun cikin watan Yunin bara, bayanda shugaba Trump ya kori jakadan Afirka ta kudu Ibrahim Rasool, daga kasar.

A lokacin da ake tantance shi cikin watan Oktoban bara, Ambasada Bozell yace zai tunkari aikinsa tare da girmamawa ga al’umar Afirka ta kudu, kuma yana ganin akwai damar kulla dangantaka mai dorewa duk da cewa akwai sassan da suke da sabanin ra’ayi.

Afrika, Amurka

Post navigation

Previous Post: ‘Yan Tawaye A Burkina Faso Sun Kashe ‘Yan Kasar Ghana
Next Post: Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Gana Da Shugaban Makaman Nukiliya

Karin Labarai Masu Alaka

Netanyahu Yayi Gaggawar Amincewa Da Kasafin Kudin Kasar Afrika
Shugaban Ukraine Ya Tattauna Da Trump Akan Zaman Lafiya Amurka
Kasar Rasha Ta Zargi Ukraine Da Kai Hari Gidan Shugaban Rasha Amurka
Iran Tace Farisa Zata Kai Hari Kan Mayakan Amurka Amurka
Najeriya Ta Bawa Dan Takarar Guinea-Bissau Mafaka Afrika
An Gano Kwale-Kwalen Fir’auna A Birnin Masar Afrika

Aiko Mana Sako Cancel reply

Kada ka damu, baza a wallafa adireshin imel dinka ba. Required fields are marked *

Sabbin Labarai

  • Wani Dan Ta’adda Ya Hallaka ‘Yan Makaranta A Kasar Uganda
  • Sakataren Tsaron Amurka Ya Kori Shugaban Sojin Kasar
  • Kwararru Sun Nuna Damuwa Game Da Yakin Iran
  • Za’a Kada Kuri’a A Kwamitin Tsaro Na MDD Kan Yaki
  • Kasashen Da Dama Na Neman Hanyar Cigaba Da Dakon Makamashi

Rukuni

  • Afrika
  • Amurka
  • Bidiyo
  • Kimiya
  • Kiwon Lafiya
  • Labarai
  • Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Najeriya
  • Nishadi
  • Rediyo
  • Rumbun Hotuna
  • Sana'o'i
  • Sauran Duniya
  • Shirye-Shirye
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Uncategorized
  • Wasanni
  • Babban Malamin Musulunci Sheikh Usman Kusfa Zaria Ya Rasu Labarai Da Ɗumi-Ɗuminsu
  • Majalisa A Kasar Somaliya Ta Amince Da Sauya Tsarin Mulkin Kasar Afrika
  • ECOWAS Zata Taimakawa Kasar Benin Da Dakarun Soji Afrika
  • ‘Yan Tawayen Kasar Kwango Ne Suka Kai Hari Filin Jirgin Saman Kisangani Labarai
  • Kungiyar Mata Manoma A Najeriya Ta Raba Kyautar Abinci A Gombe Afrika
  • An Sace Masu Ibada A Wata Majami’ar Ecwa A Jihar Kogi Tsaro
  • Sabon Magajin Garin New York Zai Soke Wasu Dokoki Amurka
  • Ministan Harkokin Wajen Najeriya Yayi Murabus Afrika
GTA Hausa Logo

Yadda Ake Amfani Da Bayanan Ku

A GTA Hausa, mun kuduri aniyar kare sirrin maziyarta shafukanmu. Wannan Tsarin Sirri yana bayyana irin bayanan da muke tattarawa, yadda muke amfani da su, da kuma zaɓuɓɓukan da kuke da su game da bayanan ku na sirri. Ci Gaba Da Karatu

Shafukan Mu

  • Facebook
  • (Twitter)
  • Instagram
  • TikTok
  • YouTube

Haƙƙin Mallaka © 2025 GTA Hausa - Dukkan Haƙƙoƙi Mallakinmu Ne.