Kungiyar Cigaban Al’ummar Tangale Tace Bata Goyon Bayan Kai Ziyara Wa Gwamnan Gombe
Kungiyar Cigaban al’ummar Tangale Dake Kudancin jihar Gombe, sun Nisanta Kansu daga Wasu da suka Ziyarci Gidan gwamnatin Gombe Domin Kai Ziyarar muba’ya’a Ga Gwamnan jihar. A taron Manema labarai da suka Kira sun bayyana cewa, basa tare da wannan Gwamnati ta Inuwa Yahaya tun bayan rashin adalci da akayi musu wajen nadin Mai Tangale…

