Taron Masu Mu’amala Da Kafar Facebook A Kano
Taron Wanda ya gudana a jihar Kano dake Najeriya ya tattaro sannennun Mutane Daga ciki da wajen jihar Domin Sada Zumunci a yayinda ake Cigaba da da Bikin Karamar Sallah
Amintacciyar Murya
Taron Wanda ya gudana a jihar Kano dake Najeriya ya tattaro sannennun Mutane Daga ciki da wajen jihar Domin Sada Zumunci a yayinda ake Cigaba da da Bikin Karamar Sallah
Gwamna Abba bai halarci Hawan Nasarawa ba Yadda aka gudanar da hawan Nasarawa a fadar Gwamnatin Kano wanda shugaban majalisar dokokin jihar, Hon Jibril Isma’il Falgore ya wakilci Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf tare da karbar bakuncin Maimartaba Sarki Malam Muhammadu Sanusi II
A jihar Katsina An Gudanar da Hawan sarki, Hawan Bariki da Hawan magajiya a jihar Katsina tare da manyan Baki da suka Ziyarci jihar a yayin Bikin sallah
Hawan Sallah Daga Masarautar Misau a Jihar Bauchi tare da Maimartaba Sarkin Misau Alhaji Ahmed Suleman Mni.
Hawan ya kayatar da jama’a da al’adun gargajiya masu ɗauke da armashi. Gwamnan ya yabawa Sarkin Bauchi bisa jagoranci nagari da ƙoƙarinsa wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai a jihar, tare da kira ga al’umma su ci gaba da bin doka da goyon bayan manufofin gwamnati. Hoto: Lawal Mu’azu Bauchi
Amurka ta girke jirage marasa matuki, tare da sojoji 200 a Najeriya domin su horar da sojojin kasar su kuma taimaka musu da bayanan sirri, a yakin da suke yi da ‘yan ta’adda a arewacin kasar, kamar yadda jami’an Amurka da Nigeria suka shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters. Jami’an sun ce sojojin na Amurka…
Ci Gaba Da Karatu “Amurka Ta Girke Jirage Marasa Matuki Tare Da Sojoji A Najeriya” »
farashin man fetur ya tashi zuwa Kashi 35 cikin 100 a wannan makon bayan da Isra’ila ta kai hari kan mafi girman cibiyar gas ta Iran, yayin da ita kuma Iran din ta mai da martani wajen kai hari kan cibiyoyin makamashin makwabtan ta. Tarayyar Turai tayi kira ga ‘yan kungiyar ta da su cike…
Ci Gaba Da Karatu “Sakamakon Rikicin Gabas Ta Tsakiya Farashin Mai Ya Karu” »
Iran tace Isra’ila ta kai hari kan cibiyar makamashin nukiliyan ta na Ahmadi Roshan a Natanz a safiyar Asabar. Kwararru a bangaren fasaha sun ce babu alamar digar guba daga makamashin, kuma mazauna kusa da wurin basa cikin hadari. Isra’ila tace bata da masaniya kan harin, yayin da Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) tace…
Ci Gaba Da Karatu “Isra’ila Ta Kai Hari Cibiyar Makamashin Nukiliyar Iran” »
Donald Trump yace Amurka na tunanin janye yaki da Iran, yayin da Iran da Isra’ila ke ci gaba da musayar hare-hare a ranar Asabar. Tasoshin yada labarai a Iran sun ce an kai hari cibiyar makamashin nukiliyan ta na Nantaz. A wani sako da ya wallafa a kafar sada zumunta, Trump yace Amurka na gab…
Ci Gaba Da Karatu “Shugaba Trump Yace Amurka Zata Janye Yaki Da Iran” »